Gwamnatin Jihar Anambra tayi kira ga duk masu gudanar da ayyukan tallafi su bada muhimmanci kan tsaro da lafiyar mabukata domin kaucewa faruwar hatsarori masu kama da turmutsutsin da ya faru a Okija, ฦaramar hukumar Ihiala.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Anambra, Mista Christian Aburime, ya fitar, gwamnan jihar, Farfesa Chukwuma Charles Soludo, ya bayyana damuwarsa kan rashin tsaron da ya haifar da wannan mummunan alโamari.
Sanarwar ta ce: โGwamnatin Jihar Anambra tana kira ga duk masu rarraba kayan tallafi, musamman ga mabukata, su tabbatar da cewa an samar da tsari mai kyau da kuma ingantaccen tsaro domin kare rayuka da lafiyar masu karษar tallafin.โ
Gwamnan ya kuma jajantawa iyalan waษanda suka rasa rayukansu a turmutsutsin, musamman mata, tsofaffi, yara, da masu juna biyu. Ya ce: โWannan mummunan abin da ya faru yana jaddada muhimmancin samar da tsari mai nagarta wajen gudanar da ayyukan taimako.โ
Haka kuma, Gwamnati ta yi kira ga masu kishin alโumma da ฦungiyoyi masu gudanar da ayyukan taimako su maida hankali kan kare lafiyar mutane a yayin gudanar da ayyukansu. โTsaro da jin daษin jamaโa sune ginshiฦan da za a gina ingantattun ayyukan taimako,โ in ji sanarwar.